Isa ga babban shafi
Amurka

Ana dakon hukuncin kotu kan dokar hana baki shiga Amurka

Yau Talata, babbar kotun daukaka kara dake Amurka za ta yanke hukunci, dangane da dage haramcin umarnin Shugaban kasar, Donald Trump ya bayar na hana baki musamman daga kasashen Musulmi guda 7 shiga Amurka.

Wasu daga cikin masu zanga zangar adawa da dokar Donald Trump ta hana baki shiga Amurka, a filin jiragen sama ba birnin Los Angeles
Wasu daga cikin masu zanga zangar adawa da dokar Donald Trump ta hana baki shiga Amurka, a filin jiragen sama ba birnin Los Angeles 路透社
Talla

Yau Talata, babbar kotun daukaka kara dake Amurka za ta yanke hukunci, dangane da dage haramcin umarnin Shugaban kasar, Donald Trump ya bayar na hana baki musamman daga kasashen Musulmi guda 7 shiga Amurka.

Tun a jiya Litinin, kotun daukaka kara da ke San Francisco, ta sanar da cewa zata saurari batun a ranar Talata game da dakatar da korar bakin da Donald Trump ya yi.

Ana saran kowane bangare ya kare matsayinsa na tsawon mintoci 30, kafin hukunci kan karar.

Mai yiwu ne dai wannan shari`a ta kai gaban kotun kolin kasar ta Amurka, idan aka yi la`akari da yadda Trump ya tsaya kai da fata kan matakin kafa dokar da yayi, ganin cewa ko da kotun daukaka karar bata amince da bukatar gwamnatinsa ba, zai iya rugawa zuwa kotun kolin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.