Isa ga babban shafi
Iran

Za a hana Amurkawa shiga Iran

Iran ta ce za ta mayar da martanin da ya dace kan matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na hana Musulmi daga wasu kasashe 7 zuwa kasar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani. IRANIAN PRESIDENCY / AFP
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce za ta hana daukacin Amurkawa zuwa kasar saboda abinda ta kira cin zarafin da Amurka ta yi wa ‘yan kasar ta, har sai Amurka ta sake matsayi akai.

Rahotanni sun ce an hana ‘yan kasar Iran da Iraqi hawa jiragen da ke tafiya Amurka saboda umarnin shugaba Trump.

Kamfanonin jiragen Etihad da Emirates da Turkish airline sun ce an umurce su da kar su sayar da tikitin Amurka ga ‘yan wadanan kasashe 7 ko kuma barin 'Yan kasar ta Iran da ke dauke da fasfo din Amurka hawa jirgin da zai kai su kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.