Isa ga babban shafi
Amurka-Britaniya

Trump ya jinjinawa Britaniya kan ficewar ta daga EU

Shugaban Amurka Donald Trump ya yabi matakin da Britaniya ta dauka na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai inda ya ce matakin zai bai wa kasar zabi kan karbar baki da gudanar da hada-hadar kasuwanci.

Donald Trump da Theresa May sun gana yau a fadar White House.
Donald Trump da Theresa May sun gana yau a fadar White House. REUTERS/Jonathan Ernst//Neil Hall
Talla

Donald Trump ya fadi hakan ne a yayin da ya ke ganawa da Firaiministar Britaniya Theresa May a fadar White House a yau juma'a.

Mista Trump ya kuma kara da cewa daukar matakin ficewa daga kungiyar EU zai bai wa Britaniya damar gudanar da harkar kasuwanci ba tare da fargabar saka idon wasu kasashen Duniya ba.

Daga karshe shugabanin biyu sun yi alkawarin kulla yarjejeniyar kasuwanci don cike duk wani gibi da ficewar Britaniya za ta iya haifarwa a nan gaba.

Misis May ta kuma mika goron gayyata ga Mista Trump na ziyarar Britaniya.

Theresa May ce shugabar da ta soma kai ziyara a Amurka tun bayan da aka rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasar Amurka a makon da ya gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.