Isa ga babban shafi
MDD

Ana shirin rantsar da sabon Sakatare Janar na MDD

Yau ake sa ran rantsar da sabon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres dan maye gurbin Ban Ki-Moon da ke kawo karshen wa'adin mulkin sa.

Antonio Gutteres sabon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Gutteres sabon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya.
Talla

An shirya rantsar da sabon sakatare Antonio Gutteres a zauren Majalisar, yayin da kuma zai gabatar da jawabi ga mambobin majalisar 193 da ke halartar bikin na yau.

Jawabin sabon sakataren zai kunshi bayanai kan shirinsa na tinkarar matsalolin da ke addabar duniya da kuma bayyana irin sauye-sauye na ci gaba da zai kawo wa Majalisar da aka kafa shekaru 71 da suka gabata.

Mr . Gutteres zai dare kujerarsa ce a ranar 1 ga watan Janairu mai zuwa, wato ‘yan makwanni gabanin mika mulki ga zababben shugaban Amurka Donald Trump mai jiran gado.
An dai bayyana fargabar rawar da sabon shugaban zai taka wajen adawa da wasu manufofin Majalisar.

Kasar Amurka ce ta fi bai wa Majalisar Dinkin Duniya gudunmowar kudadde, yayin da ta ke daukar nauyin kashi 28 a duk shekara na kudin da Majalisar ke amfani da shi don tabbatar da zaman lafiya a kasashen da ke fama da rikici.

A bangare guda, ana kyautata zaton sabon sakataren zai nada Amina Muhd, minisatar muhalli ta Najeriya a matsayin mataimakiyarsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.