Tarihin sabon Sakatare Janar na MDD
Tsohon Firaministan kasar Portugal Antonio Guterres, na gab da darewa kan mukamin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya bayan kasashe 15, mambobi a kwamitin tsaro na Majalisar sun jefa kuri’a a yau Laraba, in da ya zarce abokan takararsa wajen samun yawan kuri’u.
Wallafawa ranar:
An haifi Guterres a ranar 30 ga watan Aprilun shekarar 1949 kuma ya rike mukamin Firaministan kasar Portugal daga shekarar 1995 zuwa 2002, bayan da ya shiga siyasa a shekarar 1976, a lokacin da aka gudanar da zaben demokradiya na farko a kasar bayan juyin juya halin da ya kawo karshen mulkin kama-karya na shekaru 50.
Gabanin darewarsa kan kujerar Firaminista a Guterres ya rike mukamin shugaban jam’iyyar ‘yan gurguzu.
A lokacin da yake shugabantar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tsakanin shekarar 2005-2015, jami’in ya jagorance ta wajen tinkarar matsalar ‘yan gudun hijira a kasashen Syria da Iraqi da Afghanistan.
A wancan lokacin dai, Gutteres bai yi kasa a gwiwa ba wajen yawan kiran kasashen Yamma da su zage dantse don taimaka wa ‘yan gudun hijira.
A yau ne dai mambobi 15 na kwamitin tsaro a Majalisar Dinkin Duniya suka zabe shi a matsayin sabon magatardan Majalisar bayan sun kada kuri’ar da ta bashi nasarar doke ‘yan takara guda 9 da suka hada da kwamishiniyar kasafi ta kungiyar tarayar Turai, Kristalina Georgieva ta Bulgaria.
A gobe ne dai za a gabatar da shi a zauren Majalisar don tattabar da zabensa a hukumance.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu