Isa ga babban shafi
Belgium

An zargi mace da namiji da kai hari kan 'yan sanda mata.

A wani binciken harin ta’addancin da aka kai kan 'yan sanda a kasar Belgium da kuma kungiyar jihadi ta ISIL ta dauki nauyin kai wa, a yau alhamis an gurfanar da wani namiji daya da wata mata a gaban alkalin kotun hukunta laifukan ta’addanci.

Shingen tsaro a wajen da aka kai harin  Charleroi, ranar  6 ga watan Ogusta 2016
Shingen tsaro a wajen da aka kai harin Charleroi, ranar 6 ga watan Ogusta 2016 VIRGINIE LEFOUR / BELGA / AFP
Talla

Maharin dan kasar Aljeriya mai shekaru 33 a duniya, ya rasa ransa sakamakon harbin 'yan sanda, a lokacin faruwar harin da ya kai da wuka kan wasu 'yan sanda mata 2 a garin Charleroi da ke kudancin  kasar Belgium a cikin watan agustan da ya gabata.

A karkashin binciken wannan harin dai, mutane 6 ne aka kama a ranar larabar da ta gabata, bayan gudanar da wasu jerin binciken gidaje 8 da 'yan sanda suka yi a garin na Charleroi da kewaye, inda aka kama tarin wukake.
 

A sanarwar da ofishin mai shigar da kara ya fitar ta ce, Alkalin kotun musaman kan hukunta ayyukan ta’addanci ne, ya bada umarnin gurfanar da biyu daga cikin mutanen da ake zargi,

Mai shigar da karar gwamnatin Belgium ya ce mutanen biyu da suka hada da "Sabrina Z, yar shekaru 36 a duniya da Farid L, dan shekaru 37 dukkaninsu an zarge su ne da hannu a yunkurin aikata kisan kai, a yanayi na ta’addanci
 

Sai dai kuma mai shigar da karar ya ki ya yi karin haske kan rawar da mutanen biyu da ake zargi su ka taka a harin, ko kuma alakar da suke da ita da maharin.

A ranar 6 a watan ogustan da ya gabata ne dai, wani mutum da aka shaida mai suna K.B dan kasar Aljeriya dake zaune a kasar Belgium tun cikin shekara ta 2012, ya kai hari da wuka a gaban hedkwatar 'yan sanda da ke garin Charleroi kan wasu 'yan sanda mata 2, inda a lokacin harin ya ke kabbarar "Allahu Akbar", nan take kuma ya jikkata daya a fuska daya kuma a wuya, kafin ta ukunsu ta tandare shi da bindiga inda ya cika a asibiti.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.