An samu karuwar 'yan gudun hijira a titunan Paris
Jami’ai a kasar Faransa sun ce yawan ‘yan gudun hijira da ke kwana a kan wasu titunan birnin Paris ya karu, sakamakon rushe sansanin ‘yan gudun hijira na dajin Calais.
Wallafawa ranar:
‘Yan gudun hijirar mafi yawanci ‘yan nahiyar Africa, da suka fito daga Sudan ta Kudu, sun kafa tantunansu ne a gabashin birinin Paris.
Ko da yake ba sabon abu bane ganin zaman ‘yan gudun hijira a yankin, sai dai sun karu a wannan satin daga 1,500 zuwa akalla 2,500.
Shugaban sashin kula da karbar ‘yan gudun hijira na Faransa Pascal Brice yace karuwar masu gudun hijirar a titunan Paris ba yana nufin wadanda aka kwashe daga dajin Calai sun koma wajen da zama bane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu