Birtaniya za ta fara janyewa daga Turai a watan maris
Firaministar Birtaniya Therasa May ta ce kafin watan Afrilu mai zuwa, kasar za ta fara shirin janyewa baki daya daga kungiyar Turai kamar dai yadda al’ummar kasar ta bukata.
Wallafawa ranar:
A karkashin yarjejeniyar birnin Lisbon wadda ta kafa wannan kungiya, Birtaniya na da damar fara shirin janyewa daga kungiyar daga lokacin da ‘yan kasar suka jefa kuri’a har zuwa tsawon shekaru biyu masu zuwa.
Theresa, wadda aka zaba a matsayin firaministar Birtaniya kimanin watanni uku da suka gabata, ta ce kasar na bukatar kintsawa kafin janyewa daga Turai baki daya, kuma wannan ne ya sa ta yanke shawarar fara yin hakan a karshen watan maris na badi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu