Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya da Tarayyar Turai sun samu sabani

Kasar Turkiya ta shaidawa kungiyar kasashen Turai cewar ba za ta sassauta dokokinta na yaki da ta’addanci ba, kamar yadda kungiyar ta gindaya sharadi na bai wa al’ummar kasar bizar zuwa kasashen da ke Yankin.

Shugaban Turkiya Reccep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiya Reccep Tayyip Erdogan AFP
Talla

Firaministan Turkiya Binali Yildirim ya ce Turkiya ba za ta sauya matsayinta na yaki da ‘yan ta’adda ba ganin irin jerin hare haren ta’addancin da ake samu a kasar.

Yildirim wanda ke ganawa da shugaban Majalisar Kungiyar EU Martin Schulz ya ce sun shaidawa shugabanin kasashen Turai cewar a halin da ake ciki yanzu babu yadda za su sauya dokokinsu.

Kungiyar EU dai ta kulla yarjejeniya da Turkiya a watan Maris wanda ya kunshi ba kasar tallafin kudade da kuma biza ga al’ummar kasar da ke bukatar zuwa Turai, snnan ita kuma ta hana baki ‘Yan gudun hijira kwarara don shiga kasashen da ke Yankin.

Sai dai kungiyar EU ta ce kafin aiwatar da bada bizar dole sai Turkiya ta sauya dokokinta da suka kunshi na yaki da ta’addanci da kuma yadda ta ke dirar mikiya kan ‘Yan Jaridu, malaman jami’a da kuma masu kare hakkin Bil Adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.