Isa ga babban shafi
Syria-Turkiya

Erdoghan ya lashi takobin kakkabe ISIL

An shiga rana ta biyar da dakarun Turkiyya ke ta luguden wuta a kasar Syria kan sansanonin mayakan kungiyar ISIL da ‘yan tawayen kurdawa.

AFP
Talla

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip  Erdogan ya fadi a wajen wani gangami a garin Gaziantep da ke yammacin kasar cewa sam babu kakkautawa hare-haren da Turkiya ke kaiwa sansanonin kungiyoyin ISIL da na mayaka kurdawa dake Syria, inda alkaluma ke nuna rayukan fararen hula akalla 40 aka kashe a jiya lahadi.

Wata kungiyar dake zaune a Britaniya wadda take sa idanu kan irin wainar da ake toyawa a Syria ta gaskata cewa hare-hare da Turkiya ta kai jiya a Arewacin Syria a wasu wurare biyu sun kasance mafi muni da ya kashe fararen hula.

Sai dai kuma Hukumomi a Syria sun musanta alkaluman mamatan inda suke cewa ‘yan tawaye kurdawa 25 ne suka mutu, sannan kuma sojan kasar na iyakacin kokarin kare fararen hula.

Majiyoyi na cewa fararen hula 20 aka kashe , da wasu 25 da suka jikkata a hare-haren na lahadi a garin Al-Amarneh, sannan kuma a garin Jeb el-kussa an kashe wasu 20 da jikkata 50.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.