Isa ga babban shafi
Canada

An amince jami'an tsaro Mata Musulmi su sa hijabi

Kasar Canada ta fito da wani sabon kaki na jami’an tsaro inda ta amince ‘yan sandan kasar na musamman kuma Mata Musulmi su rika sanya Hijabi yayin gudanar da ayyukansu.

Canada ta karfafawa Mata Musulmi gwiwa
Canada ta karfafawa Mata Musulmi gwiwa Reuters/AFP
Talla

Kakakin rundunar ‘yan sandan ta musamman Scott Bardsley ya ce tuni shugaban rundunar ‘yan sandan ya bada umurnin fara amfani da sabon kakin.

Bardsley ya ce hukumomin tsaron Canada sun yanke wannan shawara domin bawa kowane dan kasar hakkinsa tare da karfafa gwiwar Mata Musulmi shiga rundunar ‘yan sandan kasar ta musamman.

Wannan na zuwa yayin da hukumomi a kasar Faransa ke kafa dokokin hana mata sanya Hijabi a kasar musamman yayin linkaya a wuraren shakatawa domin fargabar kai harin ta’addanci kamar yadda suka bayyana.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.