Hollande zai gana da Paparoma
Fadar shugaban kasar Faransa tace shugaba Francois Hollande zai gana da Paparoma Francis a wannan mako kan kisan da aka yiwa shugaban mabiya darikar katolika a kasar.
Wallafawa ranar:
Ziyarar da Hollande zai kai fadar Vatican gobe Laraba ita ce zata zama ta biyu a tun bayan zamansa shugaban kasar Faransa.
Sai dai fadar shugaban ba tayi karin haske kan abinda shugabannin biyu zasu fi maida hankali wajen tattaunawa ba.
A ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata Adel Kermiche da Abdel Malik Petijean suka kutsa kai cikin dakin bauta a Faransa inda suka yanka wanishugaban darikar Katolika a gaban mabiyansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu