Isa ga babban shafi
Birtaniya

Faransa da Jamus da Italiya na ganawa kan Birtaniya

A yau litinin shugabannin Faransa da Jamus da kuma Italiya za su gana a karo na farko tun bayan kuri’ar raba gardama da aka yi a Birtaniya, domin tattaunawa kan wannan batu a birnin Berlin na kasar Jamus.

Matteo Renzi na Italiya da  Angela Merkel na Jamus da kuma François Hollande  na Faransa
Matteo Renzi na Italiya da Angela Merkel na Jamus da kuma François Hollande na Faransa AFP PHOTO / STEFAN ROUSSEAU/POOL
Talla

Francois Hollande daAngela Merkel da kuma Matteo Renzi, za su gudanar da taron share fage ne kafin wani taron da shugabannin Turai za su yi gobe talata a birnin Brussels kan wannan batu.

A yau ne shi ma Firaministan Birtaniya David Cameron zai gana da majalisar ministocinsa yayin da ya bayyana cewa zai yi murabus daga mukaminsa nan da watan Oktoba mai zuwa.

Shi kuwa Boris Johnson wanda ya jagoranci yakin ficewar Birtaniya da kuma ake ganin watakila ya maye gurbin Cameron ya ce, kasar za ta karfafa huldar dangantaka da kungiyar tarayyar Turai duk da cewa al'ummarta sun zabi ficewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.