Isa ga babban shafi
Birtaniya

Ko ya Tasirin ficewar Birtaniya a Kungiyar Turai ga Afrika?

Mutanen Birtaniya sun kada kuri’ar ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai, Ko ya tasirin wannan matakin ga dangantakar Birtaniya da Afrika mai yawan kasashe a kungiyar renon Ingila?

Birtaniya ta kada kuri'ar ficewa Tarayyar Turai
Birtaniya ta kada kuri'ar ficewa Tarayyar Turai LEON NEAL / AFP
Talla

‘Yan kasuwa da gwamnatocin kasashen Afrika ta kudu da Najeriya da Kenya sun shiga rudani a yau Juma’a bayan masu da’awar ficewa Tarayyar Turai sun samu nasara a zaben raba gardama da aka gudanar a ranar Alhamis.

Yanzu dai sai Birtaniya ta sake tattaunanwa da kasashen Afrika kan sabunta huldar kasuwanci tsakaninsu.

Babbar barazana ga kasashen Afrika bayan ficewar Birtaniya shi ne kudaden tallafin da Tarayyar Turai ke warewa na raya kasashe masu tasowa wanda Birtaniya na cikin manyan kasashen da ke bayar da kaso mai yawa. Yanzu Birtaniya ba za ta sake ware kudaden tallafin ba na kudi sama da euro miliyan 500.

Kenya na fargaba akan raguwar adadin yawan Fulawar da ta ke shigarwa a Birtaniya, saboda girman kasuwar Turai karkashin yarjejeniyar cinikayya ta Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.