Isa ga babban shafi
Amurka

Mutane daga sassan duniya za su halarci jana’izar Muhammad Ali

Ana saran dubban mutane daga sassan duniya ne za su halarci jana’izar Muhammad Ali tsohon zakarar damben duniya da za’ayi ranar juma’a mai zuwa, a gidansa dake Louisville a Jihar Kentucky.

Mohamed Ali.
Mohamed Ali. Action Images / Sporting Pictures
Talla

Iyalan Muhammad Ali sun ce tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton da Bill Crystal mai wasan kwaikwayo da dan Jarida Bryant Gumbel na daga cikin wadanda ake saran za suyi jawabi a wajen jana’izar marigayin kafin a binne shi a makabartar Cave Hill dake Louisville.

Bob Gunnel mai Magana da yawun iyalan Muhammad Ali yace marigayin mutum ne da kimar sa ta karade fadin duniya saboda haka suna saran wadanda zasu halarci jana’izar su fito daga kowanne sako na duniyan.

Gunnell yace bayan addu’oin da iyalan sa za suyi ranar alhamis, za’a dauki gawar marigayin cikin jerin gwanon jama’a ta manyan titunan Lousville, cikin su harda titin dake dauke da sunan sa da kuma Broadway inda akayi biki lokacin da ya lashe zinare a gasar Olympics.

A karshe limamin Islama zai jagoranci addu’oi kamar yadda marigayin ya bada umurni.

Muhammad Ali ya kwashe shekaru 21 yana dambe inda ya kara sau 61, ya kuma samu nasara sau 56, 37 daga cikin su dukan kwab daya.

Ya lashe manyan kambun duniya 3 da zinaren gasar Olympics.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.