Isa ga babban shafi
Interpol

Interpol na taro kan barazanar ta’addanci a Turai

An soma taron hukumar ‘Yan sanda ta kasa da kasa wato Interpol a birnin Prague na Jamhuriyar Czech kuma taron ya mayar da hankali kan barazanar ta’addanci a Turai da kuma tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasashen.

Interpol ta bayyana damuwa kan barazanar ‘yan ta’adda da ke sajewa cikin ‘yan gudun hijirar da ke ci gaba da kwarara zuwa Turai.
Interpol ta bayyana damuwa kan barazanar ‘yan ta’adda da ke sajewa cikin ‘yan gudun hijirar da ke ci gaba da kwarara zuwa Turai. @interpol
Talla

A jiya laraba ne aka bude taron kan inganta tsaro musamman barazanar ‘yan ta’adda da ke sajewa cikin ‘yan gudun hijirar da ke ci gaba da kwarara zuwa Turai.

Tun kafin soma taron, hukumar Interpol ta yi gargadin cewa masu tsauraran ra’ayi na iya amfani da masu fataucin ‘Yan gudun hijira domin shiga Turai.

Rahoton ya bayyana damuwa kan yadda fataucin ‘yan gudun hijira ta barauniyar hanya zai taimakawa masu da’awar jihadi tsallakawa zuwa Turai

Sai dai kuma zuwa yanzu babu wata hujja da ke nuna akwai alaka tsakanin masu fataucin da kuma ‘yan ta’adda.

Sai dai kuma hankalin ‘yan sanda ya raja’a kan maharan Paris da suka saje cikin gudun hijira suka tsallako Turai daga Girka suka kaddamar da hare hare a Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.