Isa ga babban shafi
NATO-Rasha

NATO na tattaunawa da Rasha kan matsalolin tsaro

Kungiyar tsaro ta NATO na gudanar da wata tattaunawa ta musamman da kasar Rasha a yau Laraba na nufin kawo karshen barzanar tsaro a yankin kasashen Balkans da kuma yadda za a magance rikici a gabashin Ukraine.Sannan bangarorin biyu zasu tabo batun ricikin Syria da Afghansitan.

Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg
Sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Wannan ne dai karon Farko da kungiyar NATO zata gana da Rasha bayan sun katse hulda tun lokacin da Rasha ta mallake yankin Crimea na Ukraine a farkon shekarar 2014.

Sai dai duk da sabanin da ke tsakaninsu kan rikicin Ukraine da kuma rikicin Syria bangarororin biyu sun amince su tattauna domin tabbatar da tsaro a yankin balkans musamman hatsarin jiragen da aka samu na Rasha da Amurka a kwanan baya

Bayan mamayar da Rashan ta yi wa Yankin Crimea dake kasar Ukraine, kasar zata gudanar da wani taro da kungiyar kawancen tsaro ta NATO dan kawo karshen barazanar tsaron da ya addabi Yankin Balkan.

Ofishin yada labaran NATO ya ce Jakadun kungiyar 28 sun fara ganawa da wakilan Rasha a Brussels domin tattauna halin da ake ciki a Ukraine, da Afganistan tare da tsara yadda zasu samu hadin kan Soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.