Isa ga babban shafi
Amurka

Dan bindiga ya bude wuta a Majalisar Dokokin Amurka

Jami’an tsaron sun yi nasarar kama wani dan bindiga da ya bude wuta a gefen zauren Majalisar Dokokin Amurka, rahotanni daga ma’aikatar tsaron kasar na cewa an kama dan bindigan tare da karfafa matakan tsaro.

Yansanda a yayin harin ta'addanci a jahar Boston a Amurka
Yansanda a yayin harin ta'addanci a jahar Boston a Amurka REUTERS/Jim Bourg
Talla

Acewar Wani wakilin kamfanin dilancin labaran Faransa na AFP ya ce an kara karfafa matakan tsaro a fadar shugaban kasar inda aka hana shiga da fice bayan wannan al'amari na bazata da ya auku a yau litinin.

Sai dai kuma a wani sako da Hukumar Yansandan kasar ta wallafa a shafin twitter ta ce ‘yan sanda su samu nasarar kama mutumin da ya kai harin bindigan tare da bayanin cewa an jikata dansanda guda daya.

Babu wani karin bayani daga mahukuntar kasar Amurka a harin yanzu dangane da dalilin wannan harin kokuma cikakken bayani akan maharin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.