Amurka za ta tura dakarunta zuwa Syria
Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da umurnin aikewa da dakarun kasar 50 zuwa Syria, karo na farko da Amurka ke tura sojojinta na kasa zuwa Syria tun daga lokacin da wannan rikici shekaru hudu da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Fadar shugaban na Amurka ta ce za a tura dakarun na musamman ne zuwa arewacin Syria domin bayar da horo ga ‘yan tawayen da Washington ke kira masu sassaucin ra’ayi da kuma hana yaduwar ayyukan kungiyar ISIS mai da’awar kafa daular musulunci a yankin.
Kakakin fadar shugaban na Amurka Josh Earnert, ya ce daukar wannan mataki ba wai yana nufin cewa kasar ta canza matsayin kan yadda take tafiyar da yaki a Syria ba ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu