Isa ga babban shafi
Girka

Kasar Girka ta koka gameda 'Yan Gudun hijira

Kasar Girka ta ce akwai alamun alkaluman ‘yan gudun hijira da bakin haure dake shiga kasar su rubanya har sau uku zuwa watan gobe, domin za su kai 70,000 saboka matakan da wasu kasashe suka dauka da zai hana tsallakawa.  

'Yan gudun Hijira na ta taka sayyada a yankin kasar Girka.
'Yan gudun Hijira na ta taka sayyada a yankin kasar Girka. REUTERS/Ognen Teofilovski
Talla

Ministan kula da Bakin Haure Yiannis Mauzalas ya fadi a tattaunawa da shi a shirin wani gidan Talabijin cewa yanzu haka akwai bakin haure da ‘yan cirani 22,000 a kasar.

Ya ce akwai wasu 6,500 da suka makale a sansanin Idomeni dake kan iyakan kasar Girka da Macedonia kuma tun makon jiya Macedonia ta ki amincewa a ketara, domin jamian ta sun bar mutane 300 ne kawai suka tsallaka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.