Isa ga babban shafi
Faransa

Rawar da Fabius ya taka a siyasar Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius ya yi murabus daga mukaminsa bayan shafe shekaru sama da 30 ana dama wa da shi a fagen siyasar kasar yayin da ya rike mukamin Firaminista yana dan shekaru 34 da haihuwa.

Laurent Fabius na Faransa
Laurent Fabius na Faransa REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Laurent Fabius dai ya kasance Ministan harakokin wajen Faransa da ake ganin ya fi fice a kasar.

Tun a 2012 ya ke rike da mukamin Ministan harakokin waje kuma a ta fuskar diflomasiya a zamaninsa, ya taka rawa wajen cimma yarjejeniyar nukiliyar Iran tare da kokarin sasanta rikicin Syria da jagorantar tattaunar barazanar ta’addanci a Afrika inda Faransa ta tura dakarunta domin wanzar da zaman lafiya.

Fabius dai shi ya jagoranci taron tattauna yarjejeniyar rage dumamar yanayi a duniya na kasashe kusan 200.

Sau 12 Fabius na kai ziyara China, kasar da ke yawan fitar da gurbataccen iska a duniya sannan ya kai ziyara India da Saudiya.

Fabius yana dan shekaru 32 ya zama dan majalisa a Faransa, yana shekaru 34 ya zama Firaminista a 1984. Wanda ya kasance firaminista na farko mai kananan shekaru a tarihin Faransa.

Fabius ya rike mukamin Ministan kasafin kudi da ministan masana’untu a zamanin mulkin shugaba Francois Mitterrand.

Bayan sanar da ficewarsa daga gwamnatin kasar a jiya Laraba, shugaba Hollande ya ma shi tayin zama shugaban kotun kundin tsarin mulki saboda tasirin shi ga siyasar kasar, amma ya ce sai a watan Maris zai karbi aikin idan al'amuransa sun daidaita.

Ana dai ganin nan gaba Fabius zai shiga takarar shugabancin Faransa wanda zai gaji Fancios Hollande.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.