Tarukan gangami domin tunawa da hare-haren da akai wa Faransa
A wannan lahadi ana gudanar da tarukan gangami a sassa daban daban na Faransa domin tunawa da cika shekara guda da mutane sama da milyan 4 suka gudanar da tarukan gangami domin nuna alhini ga harin da aka kai ginin mujallar Charlie Hebdo da kuma wani shagon Yahudawa a kasar.
Wallafawa ranar:
A birnin Paris ana kyautata zaton shugaba Francois Hollande da kuma manyan jami’an gwmanatinsa za su halarta taron gangamin na yau a cikin wani yanayi na tsaurara matakan tsaro lura da cewa har kullum kasar na fuskantar barazana daga ayyukan ta’addanci.
Faransa dai ta kaddamar da hare-hare a kan kungiyoyin ‘yan ta’adda musamman a Syria, Iraki da kuma Mali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu