Isa ga babban shafi
Faransa

Mutumin da ya kitsa harin Faransa na zaune a cikin kasar

Hukumomin kasar Faransa sun ce su na kyautata zaton cewar mutumin da ya kitsa kazamin harin da aka kai Paris Abdelhamid Abaaoud yana nan a cikin kasar bai fice ba.

Abdelhamid Abaaoud, wanda ake nema ruwa a jallo saboda harin Paris da ya hallaka mutane 129.
Abdelhamid Abaaoud, wanda ake nema ruwa a jallo saboda harin Paris da ya hallaka mutane 129. REUTERS/Social Media Website via Reuters
Talla

Babban mai gabatar da kara a kasar, Francois Mollins ya ce, jami’an tsaro sun hallaka mutane biyu a samamen da suka kai  a yankin St-Denis a jiya da asuba bayan harba harsasai sama da 5,000, yayin da suka kama wasu mutane 8 da ake yi wa tambayoyi yanzu haka.

Yau ake saran majalisar kasar za ta fara mahawara kan bukatar shugaba Francois Hollande na kara wa’adin dokar ta baci da kuma fadada dokar yaki da ta’adanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.