Firai Ministan Faransa ya biya kudin da ya kashe a kallan kwallo
Firai ministan Faransa, Manuel Valls ya rubuta takardar karban kudi a banki wato Cheque har na Euro 2,500 domin biyan gwamanati abinda da ya kashe a tafiyar kallan kwallon kafa a Jamus.
Wallafawa ranar:
Valls ya yi amfani da jirgin sama na gwamanti zuwa birnin Berlin inda ya kalli wasan karshe tare da 'ya'yansa biyu tsakanin Barcelona da Juventus a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, lamarin da ya haifar masa da suka daga ‘yan kasar lura da cewa tafiyar ta shi ce, ba ta gwamnati ba.
A cewar Valls, masoyin Barcelona, Shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ne, Michel Platini ya gaiyace shi domin tattauna yadda za a gudanar da gasar cin Kofin Turai ta shakera mai zuwa da za a yi a Faransa.
Amma duk da wannan bayanin da ya yi, bai sa ya kubuta daga caccakar da ake masa ba, lamarin da ya sa ya yi alkawarin biyan gwamanatin kasar wannan kudin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu