Isa ga babban shafi
Waterloo

An tuna yakin Waterloo a Turai

A yau alhamis manyan jami’an diflomasiyya daga kasashen Turai da dama ne suka halarci bukukuwan zagayowar cika shekaru 200 da yakin da suka gwabza a garin Waterloo da ke kusa da Brussels, yakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da dubu 40 a wancan lokaci.

An tuna Yakin Waterloo shekaru 200 da suka gabata
An tuna Yakin Waterloo shekaru 200 da suka gabata REUTERS/Yves Herman
Talla

Lamarin dai ya faru ne a lokacin mulkin daya daga cikin manyan sarakunan gargajiyar Faransa wato Napoleon wanda Sojojin Birtaniya suka samu galabarsa.

A shekara ta 1815 ne bayan dawowar Napoleon Bonaparte daga gudun hijira, rikici ya kaure tsakanin kasashen Turai, rikicin da ma su lura da a’l amuran siyasar Nahiyar ke kallo a matsayin yakin Turai da ya haifar da rarabuwar kawuna a lokacin.

Kasashen Faransa da Jamus sun aika da Jami’an diflomasiyarsu ne kawai ba tare da halartar bikin ba.

Waterloo yaki ne mai dimbin tarihi a Turai inda Dakarun Faransa karkashin jagorancin Napoleon suka gwabza fada tsakaninsu da dakarun Birtaniya 125,000 da Jamus da Belguim.

Napoléon ya tsere zuwa Saint Helena da ke yankin Yahudawa bayan Sojojin Turai sun samu galaba akansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.