Isa ga babban shafi
Ukraine

Obama ya gargadi Putin kafin soma taron Ukraine

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya gargadi shugaba Vladimir Putin cewa Rasha za ta fuskanci hukunci mai tsauri idan ba ta dakatar da taimakawa ‘Yan tawayen Ukraine ba. Wannan gargadin na zuwa ne kafin soma zaman tattauna rikicin Ukraine tsakanin Rasha da Faransa da Jamus da kuma Ukraine.

Shugaban Amurka, Barack Obama tare da Shugabar Jamus Angela Merkel
Shugaban Amurka, Barack Obama tare da Shugabar Jamus Angela Merkel Reuters
Talla

A yau Laraba ake sa ran shugabanin kasahsen Faransa da Jamus da Ukraine da Rasha za su gudanar da wani taro don warware rikicin kasar Ukraine a dai dai lokacin da ake ci gaba da zub da jinni a kasar.

Obama ya bukaci Putin ya yi amfani da zaman tattaunawar domin samo zaren warware rikicin Ukraine.

Sai dai kuma duk da kokarin samo bakin zaren warware rikicin na kasar Ukraine, ana ci gaba da kai mummunan hari da makamin roka a cibiyar sojin Ukraine da ke Kiev inda aka kasha mutane 37.

Shugaban Ukraine Petro Poreshenko ya ce a karon farko ‘yan tawayen sun kai hari cibiyar sojin kasar da ke Kramatorsk da ofishin gwamnatin Yankin.

Poreshenko ya ce harin ya kuma samu anguwar da fararen hula suke inda mutane 15 suka mutu.

Obama ya bukaci Putin ya kawo karshen goyan bayan da ya ke bai wa ‘yan tawayen Ukraine don kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe watanni 10 ana yi.

Amurka da kasashen Turai na zargin Rasha da horar da ‘yan tawayen Ukraine tare ba su makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.