Isa ga babban shafi

Girka na neman a tattauna batun bashin dake kan kasar

Sabin mahukumtan kasar Girka sun kara matsa kaimi ta fannin diplomasiya, domin neman goyon baya kan sake tattauna batun samun bashi daga kasashen dake amfani da kudin EURO a nahiyar Turai. Sai dai kasar britaniya na kallon wannan lamarin a matsayin wata babbar barazana ga tattalin arzikin duniya. Sabon Fraiministan kasar ta Girka Alexis Tsipras, yace yanzu nahiyar Turai na cikin matsalar tattalin arziki.Tsipras ya sake kalubalantar gungun masu baiwa kasar ta Girka bashi wadanda suka hada da babban bankin kungiyar tarayyar Turai da hukumar bayar da lamani ta duniya IMF, inda yace kawo karshen tsarin tsuke bakin aljihun da wadannan gungu suka dora wa kasar, wani babban ci gaba ne ga kasar kuma abinda ya dace ne a yi a ga kasashen na nahiyar TuraiTuni dai kungiyar ta tarayyar Turai ta bayyana amincewa da wasu koke koken kasar ta Girka, amma kuma tace maganar soke yarjejeniyar gaba daya bata taso ba. Sabin mahukumtan kasar ta Grika dai sun karbi mulki ne karkashin dimbin bashin da ke kan kasar, da suka da kimanin EURO billiyan 300, kwatankwacin kashi 175 cikin 100 na yawan kudaden da kasar ke samu a cikin gida. 

Fraiministan kasar Girka, Alexis Tsipras
Fraiministan kasar Girka, Alexis Tsipras REUTERS/Yannis Behrakis
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.