Isa ga babban shafi
Birtaniya

Kotun Turai ta Soki Birtaniya

Kotun kare hakin bil’adama ta Nahiyar Turai ta yi Allah wadai da matakin da Britaniya ta dauka na hana Fursunoni damar jefa kuri’a a zaben kasar. Wannan matakin da Britaniya ta dauka na hana firsunonin damar bayyana ra’ayinsu ta hanyar jefa kuri’a ya sabawa ‘yancin dan adam kamar yadda kotun Turai ta bayyana.

David Cameron, Firaministan Birtaniya.
David Cameron, Firaministan Birtaniya.
Talla

A baya ma dai kotun tace kasashen da ke da fursunonin na da damar zaban wadanda suka cancanta su jefa kuri’a a cikin wadanda ake tsare da su amma hana daukacin fursunonin damar jefa kuri’a baki daya da Britaniya ta yi ya sabawa ‘yancin dan adam.

Duk wani matsin lamba da kasar ta yi ta fuskanta, amma Britaniya ta tsaya tsayin daka akan wannan doka abin da yanzu haka ya sa kotun ta ce Britaniya ta keta hakkin biladama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.