Isa ga babban shafi
Girka

Girka na fuskantar matsalar haraji

Wasu alkalumma da gwamnatin Grika ta fitar ta bayyana cewa mutanen kasar da dama sun dai na biyan kudaden haraji wanda kuma wannan babbar barazana ce ga kasar da ke fama da bashi da tabarbarewar tattalin arziki.

masu zanga-zangar adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati a Girka
masu zanga-zangar adawa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati a Girka
Talla

Ma'aikatar kudin kasar Girka tace mutane sama da Miliyan 3 ake fuskantar matsala da su a wajen biyan haraji, kuma tun a farkon shekarar 2014 adadin wadanda basu biyan harajin karuwa ya ke yi.

Akwai matakai da gwamnatin kasar ta Girka ta dauka da suka shafi karin kudaden haraji da kuma matakan tsuke bakin aljihun gwamnati bayan kasar ta samu tallafi daga kungiyar Tarayyar Turai da asusun lamuni.

Saboda wannan matsalar kuma Gwamnatin Girka na neman karin wa'adin da aka dibar ma ta domin samun damar daukar matakai kafin wa’adin ya cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.