Isa ga babban shafi
Kungiyar Tarayyar Turai

‘Yan takarar shugabancin kungiyar tarayyar turai sun fara muhawara

A yau litinin, manyan ‘yan takara hudu dake neman shugabancin kungiyar tarayyar Turai a karo na farko, sun fara tafka wata mahawara a jami’ar Maastricht dake kasar Hollande, yayin da ya rage sauran makwanni hudu a gudanar da zaben.

Zauren kungiyar tarayyar Turai
Zauren kungiyar tarayyar Turai REUTERS/Vincent Kessler
Talla

Mahawarar wacce ake haskawa ta kafar telebijin, da nufin shawo kan masu zabe kimanin miliyan 400 na nahiyar ta Turai, na faruwa ne a dai dai lokacin da yankin ke fuskantar barazanar tsaro dangane da rikicin kasar Ukraine.

Rahotanni sun nua cewa muhimmai daga cikin batutuwan da ake mahawarar akai sun hada da batun tsaro, tattalin arziki da kuma ci gaban yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.