Isa ga babban shafi
Brussels-Amurka

Batun Ukraine zai mamaye ziyarar Obama a Brussels

Shugaban Amurka Barack Obama ya kai ziyarar farko a hedikwatar Kungiyar kasashen Turai Brussels kuma batutuwa da ake sa ran zasu mamaye zaman taron bangarorin biyu sun hada da makomar Ukraine bayan Rasha ta karbe yankin Crimea da tattauna huldar kasuwanci tsakanin Amurka da Turai.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya isa Brussels
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya isa Brussels REUTERS/Laurent Dubrule
Talla

Obama zai gana da shugabanin Kungiyar Turai Herman Van Rompuy da Jose Manuel Barroso inda batun Ukraine zai mamaye zaman tattaunarsu a Brussels.

Tuni kasashen Amurka da Turai suka kakabawa wau manyan Jami’an gwamnatin Rasha da Ukraine Takunkumi saboda Crimea.

A taron kasashe bakwai masu karfin tattalin arzikin Duniya birnin Hague, kasashen sun dauki matakin mayar da Rasha saniyar ware inda suka soke halartar taron G8 da aka shirya gudanarwa a Sochi na kasar Rasha.

Kasashen yanzu sun mayar da taron a Brussels.

Tasirin Takunkumi

Tun lokacin da aka fara lankayawa wasu manyan Jami'an gwamnatin Rasha takunkumin, darajar kudi da hannayen jarin kasar suka dan fadi yayin da kuma manyan kamfanoni masu auna karfin biyan bashin Rasha suka ce darajar kasar ta rikito kasa.

Sai dai kuma takunkumin akan Rasha ya shafi kudin euro na kasahen Turai inda darajar kudin ta fadi a a ranar Talata a yankin Asia saboda 'Yan kasuwa sun shiga fargaba da rashin tabbas ga barazanar da kasashen yammaci ke shirin karfafa takunkumi akan Rasha saboda Crimea.

Akwai alakar kasuwanci mai karfi tsakanin kasashen Turai da Rasha, kuma masana suna ganin idan har Rasha ta katse ba su Mai, hakan zai shafi faduwar darajar euro.

Ana ganin Rasha ita ma zata dauki mataki mai kama da wanda kasashen Turai suka dauka akan manyan jami'anta

Amma matakin da yanzu ake jira shi ne ko kasashen Turai da Amurka zasu karfafa takunkumin tattalin arziki akan Rasha.

Masana dai suna ganin Turai sai sun yi taka tsan-tsan da Rasha saboda tana cikin manyan kasashen da suke dogaro wajen samun arzikin makamashi, idan kuma ba haka ba, zasu shiga wani hali.

Yanzu haka kuma mutanen yankin Crimea sun fara amfani da kudin Ruble na Rasha, kodayake rahotanni na cewa har yanzu da kudin Ukraine ne ake hada hadar kasuwanci a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.