Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine-Amurka

Al’ummar Cremea sun zabi hadewa da Rasha

Sakamakon zaben raba-gardamar da akayi a Crimea da ke kasar Ukraine, ya nuna cewar al’ummar kasar na bukatar hadewa da kasar Russia, duk da sukar matakin da kasashen duniya keyi, sai dai kasar Amurka ta ce sam bata amince da sakamakon zaben ba

Zaben Cremea
Zaben Cremea en.wikipedia.org
Talla

Sakamakon zaben ya nuna abinda da ma aka dade ana hasashe, ganin cewar akasarin mutanen da ke Yankin Crimea Rashawa ne, inda sama da kashi 95 suka amince da bukatar hadewa da kasar Russia.

Ganin yadda sakamakon ya kaya, shugaban rikon kwarya na Yankin ya ce zai mika takardan bukatar su ta hadewar da Rasha a dai dai lokacin da shugaba Vladimir Putin na Rasha ke cewar zai amince da matsayin mutanen Crimea.

Shugaba Barack Obama ya tattauna da takwaransa na Russia Vladimir Putin, inda suka sanar da sakamakon tattaunawar mabanbanta masu karo da juna.

Yayin da Putin ke cewa sun amince su lalabo hanyar tabbatar da zaman lafiya a Ukraine, shugaba Obama na Amurka kuwa, cewa yayi Amurka da kasashen Duniya ba za su amince da sakamakon zaben ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.