Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka za ta kara aikawa da jiragen yakinta zuwa Poland

Kasar Amurka za ta aike da wasu jiragen yakinta samfurin F-16 guda 12 a Ranar Alhamis ta wannan mako zuwa kasar Poland, a daidai lokacin da musayar zafafen kalamai tsakanin Rasha da kuma kasashen yamma ke dada zafafa dangane da rikicin kasar Ukraine

Jirgin yakin Amurka F-16
Jirgin yakin Amurka F-16 en.wikipedia.org
Talla

Dama dai Amurkan na shirin ganawa ne da hukumomin kasar Ukraine domin tattauna yanda ya kamata a fitowa kasar Rasha da ake zargi da ci gaba da mamaye yankin Cremea ta hanyar aike da Dakarunta a yankin.

Sakataren tsaron Amurka Chuck Hagel da takwaransa na Poland Tomaz Siemo-niak, sun bayyana cewa a jiya lahadi ne aka soma aikewa da Karin sojojin Amurka zuwa Poland, kuma za’a ci gaba da wannan aiki har zuwa ranar Alhamishin wannan Makon.

Babban Kwamandan Dakarun NATO General Philip Breedlove kuma, ya sanar da shirya ganawa da shugabannin harkokin tsaro na tsakiya da gabashin Nahiyar Turai kan wannan batu, kamar yansa sakataren tsaron Amurkan ya bayyana.

Yanzu dai Amurka na da ‘yar karamar Tawagar Dakarunta da ke a akalla kananan sansanonin Yaki 10 domin taimakawa kasar Poland horas da Dakarunta a yayin da NATO ke ta gudanar da Sintiri a Sararin Estonia da Latvia da Lithuania shekaru 10 da suka gabata.

Dama dai kasar Amurka ta dakatar da huldayyar Soji da kasar Rasha domin nuna mata rashin amincewa da mamayar da take a Ukraine.

Amurkar dai ta dakatar da horo, da musayar Dakaru da fasahohin Yaki tsakaninta da rasha dangane da wannan batu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.