Isa ga babban shafi
Faransa

Bafaranshen da aka sace a Kamaru ya isa Paris bayan sakinsa

Georges Vandenbeusch, wani malamin Kirista da Mayakan Boko Haram a Najeriya suka sace a arewacin Kamaru watanni shida da suka gabata ya isa birnin Paris bayan sakinsa a ranar Talata.

Georges Vandenbeusch, da aka sace a Kamaru yana sauka saman Jirgin Sama a Birnin Paris bayan an sake shi
Georges Vandenbeusch, da aka sace a Kamaru yana sauka saman Jirgin Sama a Birnin Paris bayan an sake shi AFP PHOTO / JACQUES DEMARTHON
Talla

Georges Vandenbeusch, mai shekaru 42 yace babu wata wahala da ya sha daga hannun mayakan da suka sace shi.

A ranar 13 ga watan Nuwamba ne aka sace Vandenbeusch a arewacin Kamaru kafin a tsallaka da shi zuwa Najeriya.

Tuni kungiyar Boko Haram ta dauki alhakin sace Bafaranshen a lokacin da aka samu labarin an sace shi.

Gwamnatin Faransa, tace ba ta biya kudin fansa ko na sisin kobo ba kafin ‘yantar da Georges Vandenbeusch. Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya ce ga al’ada kasar ba ta biyan fansa a irin wannan yanayi.

Amma gwamnatin Faransa ta yi godiya ga shugaban Kamaru Paul Biya wanda tace ya taka gagarumar rawa domin ‘yantar da Bafaranshen.

Yanzu haka akwai Faransawa guda shida da aka sace a Mali da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.