Isa ga babban shafi
Jamus

Merkel ta lashe zaben Jamus

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, ta lashe zaben kasar, sai dai ta kasa samun rinjayen da zai ba ta damar kafa gwamnati ba tare da hadin kai da wata jam’iya ba. Jam’iyar Merkel ta CDU ta lashe kashi 42 na kuri’un da aka kada, kuma ana saran za ta yi kawance da Jam’iyar SPD da ta samu kashi 26 don kafa gwamnati.

Angela Merkel Shugabr gwamnatin kasar Jamus
Angela Merkel Shugabr gwamnatin kasar Jamus REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Shugaban kasar Fraansa, Francois Hollande ya aika wad a Merkel da sakon taya murna.

Merkel mai shekaru 59 na haihuwa ta yi wa Jamusawa alkawalin sauyi da zai kyautata ci gaban tattalin arzikin kasar.

Nasarar da Merkel ta samu ya nuna tana cikin manyan masu karfin fada aji a Turai musamman a wannan zamanin da takwarorinta ke shan kaye a zabukan da suka gabata a kasashensu.

Jagorancin rikicin tattalin arzikin Turai shi ne Babban muhimmin batu da Jam’iyyar Merkel ta yi dogaro da shi a yakin neman zabe da kuma ci gaban tattalin arzikin Jamus da takaita rashin aikin yi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.