Isa ga babban shafi
Fransa

An aikewa shugaban Majalisar Dokokin Faransa wasikar barazana

A yau litinin, a an aikewa shugaban Majalisar Dokokin kasar Faransa Claude Bartolone wanda dan jam’iyyar masu ra’ayin gurguzu da ke mulkin kasar ne,da wasu wasiku guda biyu, inda ta farko ke dauke da wani sinadiri da aka ce dusar harsashen bindiga ne, yayin da wasika ta biyu ke dauke da kalaman barazana a gare shi.

Shugaban Majalisar Dokokin Faransa, Claude Bartolone
Shugaban Majalisar Dokokin Faransa, Claude Bartolone
Talla

Wannan sako dai ya zo ne a daidai lokacin da Majalisar Dokokin ke shirin zaunawa don yin mahawara ta karshe a game da daftarin dokar da ke neman halasta auren jinsi a kasar, dokar da tun kafin a tabbatar da ita ta ke shan suka daga milyoyin faransawa.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa wasikun da aka aike wa Claude Bartolone, wata kungiya ce da ta shahara wajen ayyukan tarzoma a kasar ce ta aike masa da ita, kuma tun a cikin watan Maris da ya gabata ne wannan kungiya ta soma bayyana a kasar lokacin da ta aikewa Jean-Michel Gentil, alkalin da ya gurfanar da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy a gaban kotu bisa zargin sad a karbar kudade don yakin neman zabensa daga hannun wata attajira ta kasar mai suna Liliane Bettencourt da wata wasikar mai dauke da kwalfar harsashen bindiga a cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.