Isa ga babban shafi
Faransa

Majalisar Dattawan Faransa ta amince da auren jinsi daya

Majalisar Dattawan kasar Faransa ta amince da daftarin dokar da ke halasta auren jinsi har ma da izinin mallakar ‘yaya idan ma’auratan na bukata.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande REUTERS/Patrick Kovarik/Pool
Talla

Bayan da majalisar ta amince da wannan daftari a zamanta na yau juma’a,hakan na a matsayin sharewa takwarta ta wakilai fage ne domin sake yi wa dokar bita karo na biyu a daidai lokacin da al’ummar kasar ke ci gaba da gudanar da zanga-zangar kin jinin amincewa da dokar.

Matukar dai aka amince da wannan doka, to hakan na a matsayin sauyi mafi girma da aka taba yi wa dokokin zamantakewar al’ummar a kasar tun bayan 1981 lokacin da aka soke dokar hana zartas da hukuncin kisa a kasar .

A lokacin yakin neman zabensa, shugaba Francois Hollande ya yi alkawalim halsta auren jinsi a kasar, to sai dai har yanzu yana ci gaba da fuskantar suka daga shugabannin addinan musulunci da kuma kirista na kasar har ma da wasu daga cikin magoya bayan jam’iyyarsa ta ‘yan gurguzu masu tsatsauran ra’ayi,

A karshen watan Mayu mai zuwa ne dai ake kyautata zaton cewa dokar za ta soma aiki bayan da shugaban Hollande ya sanya ma ta hannu, kuma hakan zai sa Faransa ta zama kasa ta 11 a duniya da ta samar da irinta. Wasu daga cikin kasashen da suka soma aiki da ita kuwa har da Belgium, Portugal, Netherlands, Spain, Sweden, Norway da kuma Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.