Isa ga babban shafi
Turai

Masu adawa da auren jinsi sun yi zanga-zanga a Faransa

Shi dai wannan daftarin doka da ke halasta auren jinsi a Faransa tuni ya samun amincewar karamar Majalisar dokokin kasar da gagarumin rinjiye, kuma a cikin watan Afrilu mai kamawa ne za a gabatar da shi a gaban ‘yan majalisar dattawa domin neman samun tasu amincewar.

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande REUTERS/Eric Vidal
Talla

Ta la’kari da yadda daftarin ya sami amincewar karamar majalisa rokokin ba tare da wata gardama ba, wannan ya sa masu zanga-zangar suka yi hasashen cewa ko shakka babu dokar za ta sami gagarumin rinjiya hatta ma a cikin majalisar dattawan.
Masu zanga-zangar dai sun rika furta zafafen kalamai a kan gwamnatin ‘yan gurguzu da ke mulkin kasar, tare kuma da zarginta da kasa yin wani katabus dangane da matsalar rashin aiki da ta addabin al’umma, inda a maimakon ta tunkari irin wadannan matsaloli, sai gwamnatin ta shiga kirkiro dokokin marasa amfani ga jama’a a cewarsu.

Tun da farko dai ‘yan sanda ne suka haramta wa masu shirya zanga-zangar izinin shiga har a cikin fadar shugaban kasar ta Elysee saboda a cewarsu hakan zai iya kawo cikas ga kwanciyar hankalin jama’a, to amma dai duk da haka wadanda suka shiga zanga-zangar, sun yi cincirindo a gaban Elysee suna cewa mu aiki mu ke bukata amma ba dokar halasta auren jinsi ba.

Shi dai shugaban kasar ta Fransa Francois Hollande, a lokacin yakin neman zaben shugabancin kasar, duk da cewa bai ambaci kalmar auren jinsi ba, to amma dai ya rika cewa, ‘’auren domin kowa da kowa’’.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.