Isa ga babban shafi
Girka

Gwamnatin kasar Girka ta Jaddada Mahimmancin Matakan Tsuke Bakin Aljuhu

PM kasar Girka Lucus Papademos ya yi gargadin karshe cewa muddun majalisar dokokin kasar ta yi watsi da shirin tsuke bakin aljuhu harkokin rayuwar ‘yan kasar zasu sukurkuce.Yayin jawabi ta tashar talabijin PM ya bayyana yadda kasar ke bukatar wannan shiri, wanda zai janyo mata samun kudaden da suka kai Euro bilyan 13 daga Tarayyar Turai da IMF.

Prime Ministan Girka, Lucas Papademos
Prime Ministan Girka, Lucas Papademos Reuters / Yannis Behrakis
Talla

Tuni majalisar zartaswar kasar ta amince da shirin, amma ministoci biyar sun yi murabus, yayin kunyiyoyin kwadago suka kaddamar da yajin aikin kwanaki biyu tare da ftito na fito tsakanin masu zanga zanga da jami’an tsaro.

 

Tilas shirin ya samu amincewar majalisar dokokin kasar da ministocin kudin kungiyar kasashen Tarayyar Turai kafin kasar ta cimma burin da ta saka a gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.