Isa ga babban shafi
Italiya

Kamfanin Jirgin ruwan Italia yace kuskure aka samu

Kamfanin katafaren jirgin ruwan Italiya wanda ya yi hadari da mutane sama da 4,000, yace matukin jirgin ya yi kuskure ne, abinda ya haifar da hadarin. Kamfanin yace, Kaftin Francesco Schettino, yanzu haka yana hannun jami’an tsaro, bisa zarginsa da kaucewa bin dokar kare lafiyar al’umma, matakin day a biyo bayan zarginsa da kashe rai.

Jirgin Ruwan kasar Italia wanda ya yi hadari da fasinja a tsakiyar Ruwa.
Jirgin Ruwan kasar Italia wanda ya yi hadari da fasinja a tsakiyar Ruwa. Reuters/Giglionews.it
Talla

Ya zuwa yanzu an tabbatar da mutuwar mutane biyar, mutane 15 suka bata.

Fasinjojin sun bayyana cewa kalilan daga ciki masu jin harshen Italiyanci suka fahimci abunda da ke faruwa, tare da tabbatar da bin kwashe mutane daga jirgin da ya yi hadarin. Amarya da ango masu Amarci, 'Yan kasar Koriya ta Kudu na cikin wadanda aka gano daga baya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.