Isa ga babban shafi
Girka

Boren Gama Gari Yau

Harkokin yau da kullum a yau na tsaye cik a kasar Girka sakamakon wani sabon yajin aikin gamagari saboda matakan tada komadan tattalin arziki da Gwamnatin kasar ta tsara.Harkoki da dama sun tsaya musamman sufurin jiragen sama, jiragen kasa da jiragen ruwa.Samada jiragen sama 80 aka dakatar, wasu 110 kuma aka jinkirta tashin nasu saboda maaikatar tashoshin sauka da tashin jiragen saman, sun shiga yajin aikin.Babu jiragen kasa da motocin jigilan jama'a a tituna, yayin da asibitoci da wasu ma'aikatu masu zaman kansu na rufe saboda wannan yajin aiki na kwana daya.‘Yan sanda sun fadi cewa masu boren samada 12,000 sukayi jerin gwano bisa titunan birnin Athens da wasu manyan garuruwan kasar dauke da kwalaye dake da rubuce-rubuce. 

Rbuce rubucen masu bore a Athens ranar 12 Fabrairu, 2010
Rbuce rubucen masu bore a Athens ranar 12 Fabrairu, 2010 rfi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.