Isa ga babban shafi

Akalla mutane 40 sun mutu a wata fashewar mahakar gawayi a Turkiya

Akalla ma’aikatan hakar ma’adinai 40 ne suka mutu sannan 28 suka jikkata bayan fashewar wata ma’adanar gawayi ko Kwal a yammacin ranar Juma’a a garin Amasra da ke arewa maso yammacin kasar Turkiya.

Wasu daga cikin masu aikin ceto a mahakar gawayi a Turkiyya
Wasu daga cikin masu aikin ceto a mahakar gawayi a Turkiyya REUTERS/Stringer
Talla

A cewar Ministan harakokin cikin gida, Süleyman Soylu sun kidaya shahidai 40 gaba daya, Ministan ya isa  yankin arewa maso yammacin kasar cikin dare tare da wasu jami’an gwamnati.

An ceto ma'aikatan hakar ma'adinai 58, wanda 28 daga cikinsu sun samu raunuka sakamakon fashewar da ta faru da yammacin jiya Juma'a, da dare.

Ministan Makamashi Fatih Donmez ya sanar da cewa suna gab da kawo karshen ayyukan ceto tare da sa ran ceto mutum daya, wanda har yanzu ba a san makomarsa ba.

Kafar yada labarai ta Turkiya NTV mai zaman kanta ta nuna daya daga cikin masu hakar ma'adinan da aka ceto, fuskarsa ta yi baki, wanda ya ki a kai shi asibiti cikin motar daukar marasa lafiya: y ana mai cewa  lafiyarsa lau, ina so in tsaya a nan domin in taimaka wa 'yan uwana.

Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan, wanda ake sa ran ya zo wannan wuri da abin ya faru da rana, ya sanar a shafinsa na Twitter cewa, "Hukumomin shari'a za su gudanar da bincike kan wannan mummunan hatsarin .

Shugaban kasar ya kuma yi alkawarin cewa jihar za ta dauki nauyi tare da kare iyalan wadanda abin ya shafa, musamman mutanen da aka riga aka yi jana'izarsu da safiyar yau asabar a kauyukan da ke makwabtaka da su, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.