Isa ga babban shafi
Wasanni

Shiri na musamman a kan gasar Olympics

Wallafawa ranar:

A yayin da wakilan kasashen ke kintsawa don zuwa gasar wasannin motsa jiki na Olympic da za a yi a birnin Paris na kasar Faransa a shekara mai zuwa, shirin 'Duniyar Wasanni', ya kawo tarihin gasar, inda ya yada zango a Najeriya, wadda tawagar kwallon kafarta ta 'Dream Team' ta kasance ta farko a nahiyaar Afrika da ta lashe kofin kwallon kafa a gasar Olympiic a shekarar1996.Shirin ya samu damar tattaaunawa da wasu 'yan wasa da jami'ai da aaka dama da su a lokacin.  

A birnin Paris na kasar Faransa ne za a yi gasar Olympic na shekarar 2024.
A birnin Paris na kasar Faransa ne za a yi gasar Olympic na shekarar 2024. REUTERS - CHRISTIAN HARTMANN
Talla

TARIHIN GASAR WASANNI TA OLYMPIC

Gasar motsa jiki ta Olympics an fara gudanar da ita ne a karni na 8 a kasar Girka, sai dai daga bisani aka dakatar da ita.

Bayan dakatar da gasar na tsawon lokaci, a shekarar 1940, kwamitin shirya gasar Olympics na Duniya IOC ya zabi babban birnin kasar Finland Helsinki don gudanar da gasar, amma sai dai sanadiyar barkewar Yakin Duniya na 2 aka sake dakatar ita.

Bayan kawo karshen yakin, a shekara ta 1946, IOC ya yanke shawarar sake farfado da harkar wasannin Olympics na zamani, inda aka fara gudanar da wasannin gasar a shekarar 1948 a birnin London na kasar Ingila, duk  da cewa itama ta kasance kamar sauran kasashen Turai, ta na cikin yanayi na matsi, amma sai da aka sake gina birnin na London don gudanar da gasar wasannin Olympics.

A kasar Girka aka fara gasar wasannin Olympic a cikin karni na 8.
A kasar Girka aka fara gasar wasannin Olympic a cikin karni na 8. © AP

Fiye da 'yan wasa dubu 4 ne suka fafata a wasanni 136, sai dai ba a gayyaci kasashen Japan da Jamus ba, yayin da Tarayyar Soviet da aka gayyata ta kaurace wa gasar.

Shekaru hudu bayan waccan gasar, birnin Helsinki na kasar Finland ta karbar bakuncin gasar, da aka yi wa lakabi da “gasa ta zamani”.

An fara wasanni ne a ranar 19 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 1952, wannan gasa ta Olympics wacce ita ce karo na 15, ta kasance taron wasanni mafi girma a duniya da aka gudanar bayan kammala yakin duniya na biyu.

Bayan yakin duniya na biyu, an dawo da gasar wasannin olympics amma ba a dama da Jamus da Japan ba.
Bayan yakin duniya na biyu, an dawo da gasar wasannin olympics amma ba a dama da Jamus da Japan ba. © AFP

‘Yan wasa dubu 4 da dari 955 ne suka halarci gasar daga kasashe 69, bayan maido da kasashen Japan da Jamus da wasu kasashe 13 da a karon farko ke nan suka halarci gasar, cikinsu har da Isra’ila wacce ta kasance sabuwar kasar da aka kirkira da ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya a shekarar 1948, da Vietnam da ke cikin rudanin siyasa.

Duk da cewar wannan gasar ba a farota da kasashen nahiyar Afrika ba, akwai wakilan nahiyar da suka shigo daga baya kuma suka nuna bajinta, musammanma a bangaren wasan kwallon kafa, inda a shekarar 1996 da kuma 2000 kasashen Najeriya da Kamaru suka taka rawar gani wajen lashe gasar.

A shekarar 1996 ce Najeriya ta kafa tarihin samun nasarar lashe lambar zinari a bangaren kwallon kafar gasar, lamarin daya kara karfafawa sauran kasashen nahiyar gwiwa.

A biyo mu a kashi na gaba don jin tagomashin da nahiyar  Afrika ta samu  a wannan gasa ta olympic.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.