Isa ga babban shafi
Rayuwata

Muhimmanci wayar da kan mata game da tsafta a lokacin jinin al'ada

Wallafawa ranar:

Shirin na wannan rana, ya mayar da hankali kan ranar wayar da kai game da tsaftace jikin a lokacin jinin al'ada ga mata, yayin da masana suka ayyana kwanakin na jinin al'ada a matsayin abin da ya kasu kashi daban-daban.

Audugar da mata kan yi amfani da ita lokacin jinin al'ada
Audugar da mata kan yi amfani da ita lokacin jinin al'ada REUTERS/Vincent West
Talla

Bayanai sun nuna cewa, akwai matan da suke ganin daukewar al'ada bayan kwanaki uku zuwa hudu, ko mako guda, inda wasu kuma kan dauki tsawon makonni biyu kafin ya dauke musu.

Ko da yake da zarar ya haura makonni biyu, masana lafiya sun shawarci mata da su yi gaggawar zuwa asibiti mafi kusa, domin duba lafiyarsu.

Mata da dama a wasu lokutan sukan fuskanci rashin lafiya, a lokacin da za su fara ganin al'adar  a kowanne wata, ko dai kwanaki biyu gabannin zubar jinin ko kuma idan su na tsaka da yi.

Kan wannan batu ne, Zainab Ibrahim ta shirya shiri na musamman, domin jin matakan da ya kamata mata su rika dauka wajen kula da lafiyar su.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.