Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Har yanzu 'yan kasuwar Najeriya ba su fara samun dala da sauki ba

Wallafawa ranar:

Kusan watanni biyu kenan da shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ci gaba da bai wa ‘yan kasuwa da ke shigar da wasu kayayyaki fiye da 40 a cikin kasar damar samun dala cikin sauki daga babban bankin kasar, amma har yanzu bincike na nuni da cewa ba a fara aiwatar da umurnin ba. 

Nairar Najeriya da dalar Amurka
Nairar Najeriya da dalar Amurka REUTERS - AFOLABI SOTUNDE
Talla

To sai dai a daya bangare an wayi gari da karin kudaden da ‘yan kasuwa ke biya a matsayin fito ko kuma harajin shigar da kaya a kasar ne saboda an bari kasuwa ta aikinta a fagen canjin Naira zuwa kudaden ketare.

Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Alhaji Zubairu Mele Abba-Ganamma, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu aikin fito wato 'Transit Agents', wanda ya yi mana karin bayani a game da hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.