Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Sharhin masana kan shirin Saudiyya na gyara matatun man Najeriya

Wallafawa ranar:

Kasar Saudiyya ta ce zata zuba jari a matatun man Najeriya guda 4 da yanzu haka ake gyarawa domin ganin sun dawo aikin tace mai gadan gadan, domin rage dogaro da man da ake shigo da su daga kasashen ketare. Saudiyar ta sanar da haka ne bayan tattaunawar da aka yi tsakanin Yarima Muhammad bin Salman da shugaba Bola Ahmed Tinubu a birnin Riyadh, inda aka gudanar da taron Saudiya da shugabannin Afirka. 

Mazauna yankin Neja Delta mai arzikin Mai yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale kusa da matatun mai mallakar kamfanin mai na Mobil a tsibirin Bonny. 17/8/2006
Mazauna yankin Neja Delta mai arzikin Mai yayin da suke tafiya cikin kwale-kwale kusa da matatun mai mallakar kamfanin mai na Mobil a tsibirin Bonny. 17/8/2006 ASSOCIATED PRESS - GEORGE OSODI
Talla

 

Baya ga zuba jarin a matatun man, Saudiyar ta kuma ce zata taimakawa Najeriya da kudaden dala domin rage karancinsa da ake fuskanta da kuma ceto naira dake ci gaba da faduwa. 

Dangane da wannan ci gaba, Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da masanin harkar mai da iskar gas a Najeriya, Injiniya Kelani Muhammad, kuma ga yadda zantawarsu ta gudana. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.