Dakta Abba Sadiq mazaunin Faransa kan zanga-zangar da ke faruwa a kasar
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:40
An samu saukin tarzomar da dubban Faransawa ke yi, bayan shafe kwanaki 6, suna zanga-zangar da ta kazance, biyo bayan kashe matashi da wani jami’in dan sanda ya yi. Tun daga ranar Larabar da ta gabata ne dai aka fara samun sassaucin tashin hankalin, inda kididdiga ta nuna cewar mutane 150 jami’an tsaro suka cafke, sabanin masu zanga-zanga sama da 700 da aka a ranar Asabar.
Bayanai sun ce motoci sama da dubu 2 masu tarzomar suka kone a Faransa, tare da lalata gine-gine sama da 500.
Kan wannan zanga-zanga da wasu lamuranna da suka shafe ta Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dakta Abba Sadiq mazaunin kasar ta Faransa.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakkiyar tattaunawar......
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu