Zanga-zangar Faransa: Magadan Gari sun yi bore
Magadan Gari a Faransa sun yi wani zama domin nuna adawa da zanga-zangar da aka shafe tsawon mako guda ana gudanarwa biyo bayan kisan gillar da wani dan sanda ya yi wa matashin nan mai suna Nahel, dan shekaru 17.
Wallafawa ranar:
Bayanai na nuni da cewa, zanga-zangar ta soma lafawa bayan da gwamnatin Faransar ta matsa kaimi wajen dakile masu boren da suka yi ta kone-kone da fashe-fashen shaguna.
A yau Litinin da aka shiga rana ta shiga da gudanar da zanga-zanga, Magadan Garin Faransa sun yi kira ga al’ummar kasar da su koma kan turbar mutanta dokoki bayan da masu zanga-zangar suka kaddamar da hari kan gidan wani Magajin Gari a daura da birnin Paris.
Yanzu haka dimbin jama’a ne suka fito a yau domin nuna goyon bayansu ga Magadan Garin da sauran gwamnatocin kananan hukumomi da ake kai musu farmaki da sunan zanga-zangar.
A kokarinta na magance daya daga cikin manyan kalubalen da shugaba Emmanuel Macron ke fuskanta a gwamnatinsa, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Faransa ta girke jami’an ‘yan sanda dubu 45 da suka hada da jandarmomi a dukkanin fadin Faransa a cikin daren da ya gabata.
Yau ne dai masu bincike na cikin gida suka fara gudanar da bincike kan yadda dan sandan ya dirka wa Nahel harsashi a daidai lokacin da yake tukin mota ba tare da lasisi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu