Khalifa Dikwa kan sanarwar sojoji na samun nasara kan Boko Haram da ISWAP
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:46
Shalkawatar tsaro ta Najeriya ta ce jami’anta da ke aikin a karkashin Operation Hadin Kai, ta kasahe mayakan Boko Haram da ISWAP 42 a cikin makonni biyu da suka gabata a shiyar arewa maso gabashin kasar.
Jami’in yada labarai na shalkwatar tsaron Bernard Onyeuko ya kuma sanar da cewa, akwai mayakan kungiyoyin da iyalansu dubu 3 da dari 858 ciki harda kwamandojin su 6 da suka mika wuya a garin Gwoza na jahar Borno.
Da ya ke wannan ba shine karo na farko da rundunar ke samun irin wannan nasarar ba, ko ta yanzu a iya cewar ta sha banban da na baya? Tambayar ke nan da Khamis Saleh yayiwa Farfesa Khalifa Dikwa masanin harkar tsaro a Najeriya...
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu