Yadda muka yi rayuwa a hannun 'yan bindiga da suka yi garkuwa da mu - Dayyabu
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:05
A karon farko karin fasinjojin jirgin kasa guda bakwai da 'yan bindiga suka sako a karshen makon da ya gabata bayan kwashe fiye da kwanaki 100 a tsare, sun bayyana halin da suka tsinci kansu, inda suka koka kan yadda ba sa iya ko barci domin tunawa da sauran fasinjojin da ke hannun 'yan bindigar.
Muhammad Dayyabu wanda aka fara sako matarsa da ke dauke da juna biyu, na cikin wadanda aka sako, ya kuma yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi duk me yiwuwa wajen ganin an sako sauran wadanda suka rage cikin gaggawa.
Ya dai fara ne da bayyanawa wakilinmu da ke Kaduna Aminu Sani Sado halin da suka tsinci kansu a ciki bayan da aka yi garkuwa da su a cikin jirgin kasa akan hanyar Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu